1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Isra'ila na binciken harinta.

June 14, 2010

Bnciken Isra'ila na harin da ta kai aka jiragen ruwa na agaji ga Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/Nqfp
Hannayen wani ɗan faftukar kare haƙƙin Falisɗinawan Gaza.Hoto: AP

Ƙasar Isra'ila ta ce wani komiti mai zaman kansa zai gudanar da bincike akan harin da dakarunta suka kai akan ayarin jiragen ruwan nan da ke ɗauke da kayan gaji zuwa zirin Gaza. Binciken wanda wani alƙalin Isra'ila mai ritaya zai jagoranta zai haɗa ne da wasu manyan jami'an ƙetare. Ƙasar ta Isra'ila na shan suka ne da kakkausan harshe daga dukkan kusurwowin duniya sakamakon harin, wanda a yayinsa 'yan fafutukar kare haƙƙin Falisɗinawa guda tara suka rasa rayukansu. A cikin martanin da ya mayar game da wannan sanarwa ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce ba za su amince da duk wani bincike da Isra'ila kanta za ta gudanar ba. 'Yan ƙasar Turkiya guda takwas da wani Ba'amirke da asalin wannan ƙasa ne suka mutu a ciki harin.

Mawallafiya. Halima Balaraba Abbas

Edita: Muhammad Nasiru Awal