1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia ya rage yawan dakarun shiga tsakani a iyakokin Ethiopia da Erythrea

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvp

Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya yanke shawara rage yawan dakarun da ya tura , a iyakokin ƙasashen Eryhtrea da Ethiopia, daga dakaru 3.300 zuwa 2.300.

Komitin sulhu ya ɗauki wannan mataki, ta la´akari da tafiyar hawainiya, da ake fuskanta, ta fannin tabbatar da yarjejeniyar sulhu da ƙashasen 2 su ka cimma, game da batun iyaka.

Ƙasashen 2 sun maida martani yau, ga matakin na Majalisar Ɗinkin Dunia.

A ta bakin kakakin fadar gwamnatin Asmara, batun rage yawan dakaru bai dami hukokumomin ERyhtrea ba, babban batu a cewar sa shine kasawar Majalisar DinkinDunia na matsa kaimi ga Ethiopia domin ta amince da matakan yarjejeniyar da aka cimma.

Ita kuwa Ethiopia, ta zargi Majalisar Ɗinkin Dunia,da kasa cewa uhun ga Erythrea, dangane da mataikin da ta yanke na taƙaita zirga zirgar dakarun shiga tsakanin.