1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya gargadi yan kasar Cote D`Ivoire da su gaggauta zabenn Praminista

December 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvIc

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ,ya bayana damuwa

a game da kasa, samar da saban Praminista a kasar Cote D´Ivoire.

Komitin ya jaddada aniyar sa, ta sa takunkumi ,ga duk mutumen da aka samu da hannu ,a cikin dagula harakokin siyasar wannan kasa, ya kuma kira da babbar murya ga bangarori daban daban masu gaba da juna, da su gaggauta zaben Praministan, wanda zai dukkufa ba tare da bata lokaci, a shirye shiryen zabbuka kamin watan oktober na shekara mai kamawa.

Kazilika, Komitin ya bukaci shugaba Lauran Bagbo ya baiwa saban praministan cikkkaken mulki, ta yadda zai gudanar da ayyuka ba tare da tarnaki ba.