1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu ya amince da tsawaita wa´adin mulkin L.Bagbo da shekara guda

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueW

Komitin Sulhu na Malajisar Ɗinkin Dunia, ya amince da shawara ƙungiyar Taraya Afrika, wace ta tanadi ƙara wa´adin shekara guda, ga hukumomin riƙwan ƙwaryar Cote´d´Ivoire.

Saidai baki ɗaya, membobin komitin sulhun sun ce wannan shine wa´adin ƙarshen ƙarshe, da MDD, zata ba ƙasar, domin ta shirya zaɓɓuɓuka daban-daban.

Ranar talata mai zuwa ce, wa´adi na 2, da aka ba Cote d´Ivoire, ke kai ƙarshe , ba tare da an cimma nasara shirya zaɓen ba.

A cikin wani ƙuduri da ƙasar France, ta gabatar wa komitin sulhu na MDD, Praminsitan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Bany, ya samu cikkaken mulkin, da zai bashi damar shirya zaɓen, kamin ƙarshen watan oktober na shekara ta 2007, da kuma kwace ɗamara yan tawaye, da ƙungiyoyin sa kai.

Saidai tunni, magoya bayan shugaban Lauran Bagbo, sun nuna rashin amincewa, da ƙudurin na France, da su ka ɗauka a matsayin wani juyin mulki ga shugaba Bagbo.

A ɓangaren yan tawaye ma, an nuna adawa da wannan ƙuduri, saboda ya baiwa Lauran Bagbo, damar zama kan karagar mulki, har tsawan shekara guda.