1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin sulhu ya gana akan rikicin gabas ta tsakiya

November 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bucf

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gana jiya a birnin New York game da tashe tashen hankula dake ci gaba a yankin gabas ta tsakiya.

Kasashen larabawa dai suna kira da gaggauta tsagaita wuta a Gaza,wadda suka bukaci dakaru karkashin sa ido na Majalisar su kaddamar da shi.

Wakilin Palasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya zargi Israila da aikata laifukan yaki a yankin yana mai cewa ya kamata a kama wadanda suka haddasa wannan karkashin dokoki na kasa da kasa.