1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin sulhu ya kasa sanasantawa akan batun kasar Iran

March 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuQe

Zaunannun membobin komitin sulhu na MDD da kuam Jamus sun gagara magance banbance banbance dake tsakaninsu game da samarda kuduri da zai amince da irin takunkumi da zaa lakabawa kasar Iran kann shirinta na nukiliya.

A jiya asabar ne dai jamiai daga kasashen China da Rasha da Faransa,Burtaniya da Amurka da kuma Jamus sun tattauna wannan batun wajen wata ganawa ta hanyar rediyo mai hoto.

Kodayake kakakin maaikatar harkokin wajen Amurka Kurtis Cooper yace har yanzu kasashen 6 suna kan aniyarsu ta samarda wani kudiri na biyu na takunkumi kann kasar Iran.

Yace yanzu haka wakilan Amurka a MDD zasu tattauna wannan batu a birnin New York.

Kwanan nan ne dai hukumar kula da kare yaduwar makaman nukiliya ta kasa da kasa ta fito da wani rahoto cewa Iran har yanzu tana ci gaba da inganta sinadaren uraniyum da ake anfani da su wajen samarda makamashi da kuma makaman nukiliya tana mai yin kunnen uwar shegu da waadin da MDD ta diban mata na jinginar da shirin nata.