1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu ya sake tanttana batun aika dakaru a yankin Darfur

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bul7

Komitin sulhu an MDD ya sake gudanar da mahaura akan batun tura dakarun kwantar da tarzoma a yanki Darfur na ƙasar Sudan.

Ƙasashe membobin komitin, sun ƙara sharaɗin amincewar gwamnatin Khartum, kamin aika rundunar.

Ya zuwa yanzu shugaban ƙasar Sudan Omar El-Bashir na nuna matuƙar adawa da wannan batu.

Ya kuma jaddada hakan ga wakiliyar shugaba ƙasar Amurika, albarkacin ziyara da ta kai a birnin Khartum.

Yarjejeniyar da komitin sulhu ya cimma, akan batun, ta tanadi aika sojoji dubu 17, wanda za su cenji dakarun ƙungiyar tarayya Afrika, da su ka kasa tabbatar da tsaro a wannan yanki, da ke fama da riginginmu.

Jikadan ƙasar Ghana, Nana Effah-Apenteng da ke jagoranci komitin sulhu, ya tabatar da cewa ɗaukar wannan mataki, bai nufin ƙin amincewa da tantanawa da hukumomin Sudan.

A daidai lokacin da komitin sulhu, ke shirya wannan mahaura, dubunan mutane a birnin Khartum, sun shirya zanga zanga, inda su ka yi Allah wadai, da matakin tura dakarun Majalisar Dinkin Dunia a Darfur.