1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu ya yi taron gaggawa a game da Korea ta Arewa

July 6, 2006
https://p.dw.com/p/BurW

Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya kiri taron gaggawa jiya laraba, a sakamakon harbe -harben makamai masu lizzami har guda 7, da Corea ta Arewa ta yi.

Ƙasar Japon, tare da goyan bayan Amurika France, da Britania, ta shirya jerin wasu hukunce- hukunce, da ta buƙaci a ɗauka kan hukumomin Pyong yang.

To saidai, bayan mahaurorin da ta tabka a kan wannan batu, ƙasashen Rasha da China, sun nuna adawa ga matakin.

Amma sun bukaci, a hidddo sanarwar haɗin gwiwa, domin gargaɗin Corea ta Arewa, ta daina harbe -harben.

Jerin matakan hukuncin da ƙasashen su ka bukaci a ɗauka kan Corea ta Arewa, sun haɗa da saka takunkumi ga kuɗaɗen da ƙasar ta mallaka, a bankunan ƙasashen dunia.

Sannan, ƙasashe su katse hulɗoɗin ta faninn masanyar hussa´o´in soja, da na makamai tare da ƙasar.

A wani mataki na, a na magani kai na kaɓa, hukumomin Corea, sun ce muddun Komitin sulhu ya kuskura, ya ɗauki matakai , hakan zai ƙara dagulla al´ammura.

A sahiyar yau, shugaba Georges Bush na Amurika, da Praministan Japan Yunichiro Koizumi, sun bayyana haɗa ƙarfi, domin matsa lamba, ga komitin sulhu, ya hukunta Corea ta Arewa.