1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korar bakin haure daga Turai zuwa kasashensu na asali.

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2003
https://p.dw.com/p/BvnW
Rahotanni game da korar bakin haure daga nahiyar Turai na nuni da yadda batun na korar baki ke da sarkakkiyar gaske. Alal misali majalisar dokokin kasar Austriya ta amince da wata dokar da ta shafi ba da mafaka mafi tsanani a nahiyar Turai. Dokar dai ta ba hukuma damar mayar da bako kasarsu ta asali cikin sa´o´i 72 kacal. Haka zalika majalisar Turai na kakkausar suka da hanyoyin da mahukuntan kasar Finnland ke bi wajen yiwa bakin da ake shirin korarsu, allurar maganin kashe jiki. A Belgium kuma har yanzu kotun kasar na shari´a game da Semira Adamu, daga Nijeriya wadda ta rasa ranta a lokacin da ake komawa da ita gida a karkashin tilastawar jami´an ´yan sanda. Kimanin shekaru 4 da suka wuce a karon farko a nan Jamus wani dan kasar Sudan Aamir Ageeb ya rasa ransa a hannun jami´an dake tilasta komawarsa gida. A birnin Hamburg kuma, kokarin da mahukuntan wannan birni ke yi na komawa da wasu ´yan mata biyu ´yan´uwan juna wato Sylvia da Gifty Oppong gida Ghana daga hannun mahaifiyarsu dake nan Jamus, ya ta da hankalin jama´a.

Daraktar hukumar shige da fice ta kasar Ghana Elizabeth Adjei ta nuna rashin jin dadin ta game da matakan rashin imani da kasashe musamman na yamma ke dauka wajen tasa keyar bakin haure zuwa kasashen su na asali. Misis Adjei ta ce rashin tausayi ne a raba yaro karami da iyayensa bisa wasu dalilai da ba su taka kara sun karya ba. Daraktar ta ce yanzu suna nazari sosai su ga cewa a kare hakkin wadanda ake korar.

Ade Abimbola dana kasar janhuriyar Benin wanda ya shafe shekaru da dama a birnin Paris kafin ya karasa zuwa birnin New York ya kwatanta zaman baki a Turai da kuma Amirka. Mista Abimbola wanda yanzu haka ya koma gida Benin, ya ce sanda yake a kasar Faransa a kullum ji yake kamar yau ne ko gobe ana iya komawa da shi gida, amma a Amirka ko da rana daya bai taba yin wannan tunani ba, duk da cewa ya yi makwabtaka da ofishin ´yan sanda.
Mahukunta a kasashe masu tasowa na da ra´ayin cewa kamata yayi kasashen da ke korar bakin su rika daukar nauyin sake tsugunar da su a yankunansu na asali, musamman ta hanyar ba su jari da zasu fara sana´a da shi. Domin sau da yawa wadanda aka korar kan fada cikin halin rashin kudi fiye da na gabanin sun bar gida.