1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korea ta Arewa ta yi gwajim makamman nuklea

October 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bugb

Da sanhin sahiyar yau ne, Korea ta Arewa, ta yi gwajin makaman ta na nukleya, wanda ta ce ya yi nasara 100 bisa 100.

Gwajin ya wakana, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Dunia, da ƙasashe masu fada a ji, ke kira ga hukumomin Pyong Yang, su yi watsi da wannan mataki, da ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa.

Wannan al´amari, ya hadasa cece-kuce a dandalin diplomatia na dunia.

Ba da bata lokaci ba, ƙasashen Sin da Amurika sun yi Allah wadai, da gwajin wanda a cewar su ke matsayin barazana, ga zaman lahia, a yankin kudu maso gabancin nahiyar Asia, da ma dunia baki ɗaya.

A nasa gefe, komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya ce za shi nazari kamin ya yi huruci, a kan wannan saban yanayi da aka shiga.

Ita kuwa ƙasar Japon, ta tabatar da cewa mudun ya tabata Korea ta Artewa ta yi wannan gwaji to zata maida martanin da ya dace a lokacinda ya dace, kasar Japon na daga sahun kasashen da ke bukatar yin anfani da ayoyin doka ta 7, na MDD, wanda su ka tanadi yin anfani da ƙarfin soja, ga Korea ta Arewa, muddun ta mallaki makaman nukleya.

Korea ta Arewa, ta bayyana ɗaukar mataki mallakar makaman nuklkea,domin kariyar kanta, daga barazanar mamayen Amurika.