1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korea Ta Arewa ta yi gwajin harba rokokinta guda 6.

July 5, 2006
https://p.dw.com/p/BurX

Ƙasar Korea ta Arewa, ta yi wa kiran da ƙasashen duniya da dama suka yi mata, kunnen uwar shegu, ta ci gaba da aiwatad da gwajin sabbin rokokin da ta ƙera guda 6, a cikinsu har da wani mai dogon zango, wanda zai iya lulawa har zuwa Amirka. Gwajin, wanda Korea ta Arewan ta yi yau, ya ƙara janyo hauhawar tsamari a yankin arewacin Asiya, kuma ƙasashen yankin da Amirka sun yi kakkausar suka ga mahunkuntan birnin Pyongyang. Rahotannni dai sun ce dukkan rokokin da aka harba, sun faɗo ne cikin tekun Japan. Jami’an Amirka, waɗanda suka sa ido kan harba rokokin sun ce, rokar mai dogon zango, wanda aka yi wa suna Taepodong-2, ta yi kuskure na sakan 40, bayan da aka harba ta. Ita dai Amirka, ta yi barazanar cewa idan Korea Ta Arewan ta sake yin wannan gwajin, wanda take gani kamar tsokana ce, to za ta ɗau duk matakan da suka dace wajen kare kanta da kuma abokan burminta da ke yankin. Ƙasar Japan kuma, ta bukaci taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, don ya tattauna abin da ta kira wannan tsokana ta Korea Ta Arewan.