1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korea Ta Kudu ta ce gwajin rokokin da maƙwabciyarta ta arewa ta yi, zai gurgunta hulɗoɗi tsakaninsu.

July 5, 2006
https://p.dw.com/p/BurY

Da yake mai da martani ga gwajin rokokin da Korea Ta Arewa ta yi, ministan harkokin wajen Korea Ta Kudu, Ban Ki-moon, ya ce shawarar da mahukuntan birnin Pyongyang suka yanke na yin wannan gwajin, wato barazana ce ga harkokin tsaron yankin arewacin Asiya gaba ɗaya, kuma hakan zai janyo wani gagarumin cikas ga hulɗoɗi tsakanin ƙasashen biyu. Ministan dai bai bayyana irin matakan da ƙasarsa za ta ɗauka ba, amma ya ce halin da Pyongyang ta nuna zai ƙara mai da ita saniyar ware.

An dai sami sassaucin tsamari tsakanin ƙasashen biyu na Korea a ciikin shekarun bayan nan. Kuma har ila yau, Korea ta Arewa ta dogara ne kan samun taimakon abinci daga Kudu, don ta iya ciyad da al’ummanta. A wannan shekarar ma, sai da ta bukaci tan dubu ɗari 5 na shinkafa daga Kudu, sai dai har ila yau, mahukuntan birnin Seoul ba su ba ta amsa ba tukuna.