1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi barazana kan makamai

May 19, 2017

Ba za mu fasa kera makamai masu linzami ba, matukar Amirka ta ci gaba da yi mana barazana, inji jakadan Koriya ta Arewa a Majalisar Dinkin Duniya Kim In Ryong.

https://p.dw.com/p/2dGth
Nordkorea Kim Jong Un schaut sich die balistische Rakete Hwasong-12 an
Hoto: Reuters/KCNA

Mataimakin jakadan Koriya ta arewa a Majalisar Dinkin Duniya yace kasarsa za ta gaggauta cigaba da bunkasa karfin makamanta na nukiliya matukar Amirka ta cigaba da nuna mata manufofin kiyayya.

Kim In Ryong ya kuma yi watsi da zargin cewa Koriya ta arewa na da hannu a kutsen da aka yi na satar shiga yanar gizo da cewa kalamai ne na wauta.

Yace a duk lokacin da wani bakon abu ya faru Amirka kan nuna irin wannan halayya ta kiyayya ta kaddamar da farfaganda da gangan tare da danganta Pyongyang da lamarin.

Yace idan gwamnatin Trump na bukatar zaman lafiya a yankin tsibirin Koriya to ya kamata ta maye gurbin yarjejeniyar da ta kawo karshen yakin koriya ta 1950 zuwa 1953 da yarjejeniyar zaman lafiya ta kuma dakatar da manufofinta na kin jinin Koriya ta arewa.