1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta arewa ta yi barazanar yin wasu gwajin makamai

July 7, 2006
https://p.dw.com/p/BurM

ƙasar Koriya ta arewa ta baiyana a yau cewa gwajin makamai masu linzami da ta yi ba hari ne ta kai a kan wani ba, a saboda haka ta ce babu wata hujja da zaá nemi a tsamgwame ta. A yau ɗin kuma jakadan Amurka Christopher Hills ya isa yankin na Asia domin ƙarfafa matsayin Amurka cewa wajibi ne a jawo hankalin Pyongyang domin ta shiga taitayin ta. Amurkan dai ta gaza samun goyon baya a yunkurin ganin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya zartar da ƙudiri a kan koriya ta arewa bisa gwajin makaman masu linzami. ƙasashen Rasha da China sun soki lamirin yin tofin Allah tsine ga koriya ta arewa a maimakon hakan sun bukaci a yi mata jan kunne ne kawai. Koriya ta arewan ta yi barazanar cewa idan aka matsa mata tana iya yin gwajin wasu makaman a nan gaba. Shugaban Amurka George W Bush ya ce wajibi ne kasashen duniya su dauki mataki na bai daya a kan ƙasar Koriya ta arewa wadda yace tana wuce gona da iri. A nasa ɓangaren shugaban ƙasar Sin Hu Jintao ya shaidawa shugaban na Amurka cewa ƙasar Sin bata goyon bayan dukkan wani abu da zai kawo rashin kwanciyar hankali a yankin.