1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi wa Amirka gargadi

April 23, 2017

Koriya ta Arewa ta ce a shirye take ta kakkabe jiragen yakin Amirka a wani mataki na tabbatar wa Amirkar da karfinta na soji. Kasar ta kuma kame wani dan Amirka yayin da yake kan hanyarsa ta ficewa daga kasar.

https://p.dw.com/p/2blTd
Nordkorea provoziert mit weiterem Raketentest
Hoto: Gettty Images/AFP/E. Jones

Barazanar Koriya ta Arewa na wannan Lahadi, na zuwa ne daidai lokacin da wasu jiragen ruwa na kasar Japan biyu ke wani atisaye da jiragen yakin Amirka a yankin yammacin Pacific. Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin wasu manyan jiragen kasar su keta gabar ruwan yankin na Koriya, a martaninta kan yunkurin Koriya ta Arewa na gwada makaman nukiliya da masu linzami.

Ba a dai bayyana takamaiman wuraren da Amirkar ke hari ba a yankin, sai dai kalaman mataimakin shugaban Amirka a jiya Asabar na cewa nan ba da jimawa ba ne jiragen za su isa.

Koriya ta Arewar ta kuma kama wani dan kasar Amirka da ke kokarin ficewa daga kasar a wannan Lahadin, bayan kasancewar wasu Amirkawan biyu da ke tsare tun farko.