1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu: Kuri'ar yiwuwar tsige shugaba

Zainab Mohammed Abubakar
December 9, 2016

Majalisar dokokin kasar na kada kuri'ar tsige shugaba Park Geun-Hye, saboda alaka da Choi Soon-Si, da ke fuskantar shari'a.

https://p.dw.com/p/2Tzec
Südkoreas Parlament entscheidet über Amtsenthebung von Präsidentin Park
Hoto: picture-alliance/dpa/Yonhap

'Yan majalisar dokoki bangaren adawa sun gabatar da bukatar fara shirin tsige shugaba Park Geun-Hye ta kasar Koriya ta Kudu, wanda ke share hanyar kada kuri'a kan hakan.

Ana bukatar kashi biyu daga cikin uku na kuri'un 'yan adawa da membobin jam'iyya kafin samun nasarar tsigeta, Bayan boren da ya tilastawa masu shigar da kara daukar mataki akan shugaba Park, saboda neman shawarar abokinta Choi Soon-Sil.

Choi dai yana zaman jiran shari'a dangane da zarginsa da wasu laifuffuka na sabawa gwamnati. Idan an cimma tsigeta, kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudun nada wa'adin kwanaki 180 na tabbatar da kawo karshen mulkin shugaba Park.