1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Faransa ta rufe shari'ar mutuwar Yasser Arafat

Gazali Abdu TasawaSeptember 2, 2015

Kotun ta dauki matakin rufe shari'ar a bisa a cewarta dalillan rashin samun kwararan hujjojin da ke nunar da cewa wasu suka kashe jagoran Palasdinawan ta hanyar bashi guba.

https://p.dw.com/p/1GQHc
Yassir Arafat
Hoto: Getty Images

A Faransa a wannan Laraba lauyoyin da ke kare iyalan tsohon jagoran Palasdinawa marigayi Yasser Arafat sun ce alkalan da ke da nauyin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsa sun bada umarnin rufe shari'ar kwata-kwata a bisa a cewarsu dalillai na rashin samun kwararan hujjoji da ke nunar da cewa wasu ne suka kashe shi.

Mai dakin marigayi Yasser Arafat ce dai ta shigar da kara a cikin watan Agustan shekara ta 2012 tana mai zargin cewa wasu ne suka kashe mijin nata ta hanyar ba shi gubar wani sinadari da ake kira Polonium 210. Amma a cikin wata sanarwa da ya fita babban mai shigar da kara a kotun Nanterre da ke yammacin birnin Paris ya ce bincike bai gano wata hujja da ta tabbatar da hakan ba.

Ran11ga watan Novambar shekara ta 2004 ne Allah ya yi wa Jagoran Palasdinawan cikawa a wani gidan assibitin sojoji na kusa da birnin Paris na kasar Faransa bayan ya yi fama da wata 'yar gajeriyar rashin lafiya da ba a gano ko wace iri ce ba har kawo yau.