1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a jamus ta yankewa mutum na shida a duniya da ake zargi da kai hari Amurka

August 19, 2005

Ana zargin Mutassadiq da laifin yana da hannu shirya hare haren 11 ga watan satumba a Amurka

https://p.dw.com/p/BvaN
Mutassaddiq
MutassaddiqHoto: AP

An kama Montassadeq ne da laifin zama dan kungiyar Al-Qaeda, an kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru 7 gidan yari kodayake kotun ta wanke shi daga laifin yana da hannu a harin da aka kai Amurka na ranar 11 ga watan satumba.

Mai sharia Ernst Rainer yace, kotu tayi imanin cewa Motassadiq abokin huldar Muhammed Atta ne,dalibin jamiar Hamburg da ya ja daya daga cikin jiragen da suka kai hare haren a birnin New York,alkalin yace abinda suke tsammani shine, shugabanin Alqa’ida bayan gwaji da sukayi musu, sun gano cewa mutassadiq ba shi da karfin hali irin na Muhammad Atta, da zai iya kai hari irin wancan.

Yanke wannan hukunci ya zone bayan an shafe shekara guda ana sake sauraron karar wadda masu daukaka karar suke kokarin tabbatar da cewa Mutasaddiq yana da hannu a harin na 11 ga watan satumba da yayi sanadiyar mutane kusan 3000.

Wannan sabon hukunci da aka yanke ya biyo bayan samun shaida ne daga wasu fursunoni yan Alqaeda da Amurka take rike da su,shaida kuma da Amurkan ta boye a shariar farko,sai a wannan karo ta fito da su.

Washington taki yadda da kotun ta Jamus ta tambayi wadannan fursunoni saboda a cewarta, dalilan tsaro.

Daya daga cikin fursunonin Ramzi al Shaiba ya bada bayanin cewa Mutassadiq yana daya daga cikin daliban jamiar Hmaburg da suka samu horon gwagwarmaya da kuma tattunawa akan batutuwa na kin jinin Amurka,amma yace bai san kome ba a game da shirin kaiwa hare haren na Amurka.

Gwamnatin kasar Jamus dai tayi maraba da wannan hukunci,ministan harkokin cikin gida Otto Shilly yace wannan ya nuna cewa kasar Jamus tana nata yaki da taaddanci bisa dokar kasar,ya kara da cewa ganin an kama tare da hukunta dan Al qaeda a Jamaus, hakan na nuni da cewa Jamus ta sadaukar da kanta ga yakar taaddanci cikin nasara.

Shilly ya kuma baiyana rashin jin dadinsa akan yadda Amurka taki yadda suyiwa fursunonin da suka bada shaidar tambayoyi su da kansu,sai dai kawai sun dogara ne akan bayanai da Amurkan ta basu,yace ba wata hanya kuma da zasu iya bincika tabbacinsu,matsayi da yace suma alkalan Amurka suke fuskanta.

Sai dai lauyan Mutassadiq,Ladislav Anisic,yace zasu sake daukaka kara,wadda yace yana sa ran koda basu samu nasara ba dai, Mutassadiq zai yi zaman shekara daya ne kacal gidan yari kafin kuma a kore shi daga kasar jamus, ganin cewa ya dade a daure kafin a yanke masa hukunci.

Lauyan a lokacin shariar ya ja da cewa, duk da cewa Mutassdiq ya halarci wani horo na Aqaeda a sansaninsu na Afghanistan,shi mutum ne da bashi da karfin hali ko zuciya da ma ilmin da yan taadda suke da shi,yace batun taimakon gudanarda harkokin kudi ko harakar sanaoin fursunonin da suke daure da aka ce yayi kuwa, ba wani abu bane illa taimako ga yan uwansa musulmi da suke kasashen waje.

Mutassadiq yana daya daga cikin mutane shida a duniya da kaka taba yankewa hukunci ko suke jiran a yanke musu hukunci bisa laifin hannu a hare haren ranar 11 ga watan satumba.