1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Najeria ta kama shugabannin OPC da laifuka

December 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvIY

A Nijeriya,kotu ta kama shugabannin kungiyar bangarorin OPC biyu da laifin kokarin gurgunta aiyukan gwamnati da kuma mallakar makamai ba bisa kaida ba.

A watan da ya gabata ne aka sake Fredrick Faseun da Gani Adams na bangarorin Oodua Peoples Congress OPC daga gidan yari,bayan da babbar kotun Lagos ta yi watsi da tuhumar laifin kisan kai da kae musu.

Amma kuma rundunar yan sandan taraiya ta sake tsare su yayinda suka fito daga harabar kotun,aka mika su zuwa birnin taraiya Abuja nesa da mahaifarsu inda yan kabilarsu ta yoruba suka fi yawa.

A halin yanzu suna fuskantar sabbin zargi na gudanar da haramtacciyar kungiya da kuma gurgunta harkokin gwamnatin taraiyar Najeria tare da neman tada zaune tsaye da mallakar makamai ba bisa kaida ba.

Dukkan yan kungiyar 6 da ake tuhuma sun ki amsa laifukan da ake tuhumar su da su,alkali mai sauraron karar ya bukaci a mayar da su hannun yan sanda har sai ranar 6 ga watan fabrairu mai zuwa da zasu sake baiyana gaban kotu.