1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta dage shari´ar tsofan shugaban kasar Iraki

December 7, 2005
https://p.dw.com/p/BvHX

A kasar Iraki kotu ta dage sauraran shari´ar tsofan shugaban kasa Saddam Hussein, har zuwa ranar 21 ga waatn da mu ke ciki.

Saddam Hussain ya yi tawaye ga zaman kotun na yau, domin nuna fushin sa, a kan tozarcin , da rashin adalici , da a cewar sa, kotu ke nuna masa.

A zamman jiya, an saurari shaidu 5, a game da zargin da ake yi ma tsofan shugaban kasar ,na hallaka mutane 148 ,a garin Dujail, a shekara ta 1982.

Shari´ar na gudana a yayin da hare haren kunar bakin wake, ke ci gaba da kara kamari a sassa daban daban na kasa.

A sahiyar yau, yan takife su ka kai hari, ga babban assibitin birnin Kirkiuk, inda su ka hallaka yan sanda 3.

A ci gaba kuma da kiranye kiranye, domin belin mutanen da yan takifen ke garguwa da su, tsofan shugaban Jamus Geher Schröder ya roke su, da su sako bajamisar da su ka kama.

Hujar da babban alkali kotu, ya bada ta dagge wannan shari´a, na da nasaba, da yakin neman zabe, da ake ciki, a shirye shiryen zaben yan majalisar dokoki, da za a yi a mako mai zuwa.