Kotu ta jingine zaman majalisar Kataloniya | Labarai | DW | 05.10.2017

Labarai

Kotu ta jingine zaman majalisar Kataloniya

Kotun tsarin mulki a Madrid ta jingine zaman majalisar dokokin Kataloniya inda shugabannin yankin ke shirin ayyana ballewa daga Spain.

Spanische Verfassungsgericht (picture alliance/dpa/J. C. Hidalgo)

Ginin kotun tsarin mulkin Spain

Kotun tsarin mulki ta kasar Spain a ranar Alhamis din nan ta zartar da hukuncin jingine zaman musamman da majalisar dokokin Kataloniya ta kira domin tattauna ballewa daga Spain.

Jam'iyyar gurguzu ta Kataloniya PSC mai ra'ayin kasancewar yankin a cikin Spain wadda kuma har ila yau ta ke adawa da yunkurin ballewar yankin, ta shigar da karar gaban kotu tare da hujjojin cewa ayyana 'yancin kan ya sabawa kundin tsarin mulki sannan zai rusa matsayin 'yan majalisun dokokin yankin na Kataloniya.

Dakatarwar da kotun tsarin mulkin ta yi, ya zo kwana daya bayan gwamnatin hadaka ta yankin ta yi kiran ayyana ballewa a ranar Litinin mai zuwa wanda zai shata sabuwar makoma ga yankin yayin da al'ummar suka kada kuri'ar ballewa daga Spain a kuri'ar raba gardamar da suka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.
 

Albanian Shqip

Amharic አማርኛ

Arabic العربية

Bengali বাংলা

Bosnian B/H/S

Bulgarian Български

Chinese (Simplified) 简

Chinese (Traditional) 繁

Croatian Hrvatski

Dari دری

English English

French Français

German Deutsch

Greek Ελληνικά

Hausa Hausa

Hindi हिन्दी

Indonesian Bahasa Indonesia

Kiswahili Kiswahili

Macedonian Македонски

Pashto پښتو

Persian فارسی

Polish Polski

Portuguese Português para África

Portuguese Português do Brasil

Romanian Română

Russian Русский

Serbian Српски/Srpski

Spanish Español

Turkish Türkçe

Ukrainian Українська

Urdu اردو