1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta sake gurfanar da tsofan shugaban ƙasar Irak

Yahouza Sadissou MadobiAugust 21, 2006

Kotu ta sake gurfanar da tsofan shugaban ƙasar Irak Saddam Hussain bayan tuhumar sa da lefin kissan kiyasu kan Ƙurdawa

https://p.dw.com/p/Btyd
Hoto: AP

Bayan shari´ar da kotuna su ka yi wa tosfan shugaban ƙasar Irak Saddam Hussain, a game da kissan gilla, a kan mutane 148 na garin Dujail, a shekara ta 1980, yanzu kuma, kotu ta sake gurfana da shi, a kan wata sabuwar haraka.

A wannan karo, kotu na tuhumar Saddam Husain, da hannu a cikin kissan kiyasun, da ya wakana a Anfal, tsakanin 22 ga watan februaru, zuwa 6 ga watan satumber, na shekara ta 1988, inda sojoji, bisa umurnin shugaban ƙasa su ka yi anfani da makamai masu guba, da kuma bama bamai, domin hallaka a ƙalla Ƙurdawa dubu 182.

Da farkon buɗa shari´ar, Saddam Hussain yayi kunnen uwar shegu, ga tambayoyin da alaƙali Abdallah Al-Ameri ya yi masa, kafin daga baya, ya yi masa hurjin mussa, a cikin wata sa,in sa insa da su ka yi, inda alƙalin ya fara da tambayar sa kamar haka:

Ina buƙatar ka gabatar da sunan ka.

ba ka san suna na ba?

na sani, amma doka ce a aka kafa a Iraki,tun shekara ta 1969, inda alƙali ke da alhakin tambayar sunan wanda a ke tuhuma, ko da kuwa ya san shi

Ina mutunta wannan doka, to saidai kai, a matasyin da kake nan, karen farautar Amurika ne kai, ba ƙasar Iraki kake wakilta ba.

To ka dai, gabatar da sunan ka.

Ai ba za ni gabatar da suna na ba, domin kuwa, a Irak da faɗin dunia baki ɗaya, kowa ya sanni.

To bayan dai wannan sa toka sa katsi, da a ka yi , tsakanin Alƙali da Saddam Hussain,tsofan shugaban kasar, daga ƙarshe ya gabatar da sunan sa,amma a matasyin sa na shugaban ƙasa mai ciakkaken mulki, kuma shugaban rundunar tsaro.

A yayin da alƙali yayi masa tambayar ko ya na da masaniya a kann lefin da ake tuhumar sa, Saddam ya ki ya bada ansa, haka zalika, sauran mutane 6 da ake tuhumar su tare da shi.

A cikin shari´ar alƙali Abdalah Al- Ameri, ya haramta ma lauyoyin Saddam guda 2 ,su kare shi, dalilin cewar ba yan Irak bane.

Wannan mataki ya harzuƙa tsofan shugaban ƙasar.

Haka zalika, zargin cewar sojojin sa, sun yi wa mata fyaɗe.

A cikin ɓacin rai, Saddam ya bayana cewa,muddum zargin yi wa mata fyaɗe a zamanin sa,ya kasance batu mara tushe, to zai sa ƙafar wando guda, da alƙalin da ya ƙirƙiro wannan ƙage har ƙarshen rayuwar sa.

A ƙarshe al´amari dai,an tashi daga wannan shari´a, ba tare da samun wanni haske ba, a game da lefikan da ake tuhumar Saddam Hussain, kotu zata sake wani zama gobe da yamma, idan Allah ya kai mu.