1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu za ta yanke hukunci a kan zaben Gabon

Mouhamadou Auwal Balarabe/AHSeptember 23, 2016

Kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Gabon za ta yanke hukunci dangane da karar da 'yan adawa suka shigar kan sakamkaon zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1K7Ou
Bildkombo Ali Bongo und Jean Ping Gabon
Hoto: picture-alliance/dpa/E.Laurent/L.JinMan

Kasar Gabon ta wayi garin wannan Jumma'a cikin fargabar barkewar tashin hankali sakamakon hukuncin da kotun tsarin mulkin za ta ba da dangane da kararrakin bayan zabe. Batun da ya fi daukar hankali shi ne zargin da dan takarar adawa Jean Ping ya yi wa shugaba mai ci yanzu Ali Bongo Ondimba da magudin zabe, lamarin da ya ce ba za ta sabu ba. Dama yau ne ranar karshe da doka ta tsaida ta bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasar Gabon tsakanin Ali Bongo Ondimba da wanda ya kalubalanceshi Jean Ping.

Zaman fargaba na al'umma a Gabon daf da lokacin bayyana hukunciTuni dai mazuna Libreville babban birnin kasar da Port Gentil da ke zama cibiyar cinikayya suka jibge abinci a gidajensu saboda gudun abin da ka je ya zo. Ya zuwa yanzu ma dai al'amuran sun fara tafiyar hawainiya a Libreville, inda aka jibge jami'an tsaro a kewayen kotun tsarin mulki da kuma fadar shugaban kasa. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da tashin hankalin da ya barke bayan hukumar zabe ta bayyana Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 27 ga watan Agusta da ratar da ba ta taka kara ta karya ba. Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wannan rikici, yayin da dukiyoyi kuma suka salwanta.Manyan alkalai tara na kotun tsarin mulkin Gabon sun saurari bahasi daga bangarori biyu da abin y a shafa tun a ranar Alhamis.

Gabun Libreville Ausschreitungen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari