1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Arusha ta kammala sauraran Kalan Bagosora

June 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuK3

Kotun mussamman da Majalisar Ɗinkin Dunia ta girka a birnin Arusha na ƙasar Tanzania,domin yanke hukunci, ga mutanen da a ke tuhuma, da alhakin kissan kiyasun da ya wakana a ƙasar Ruwanda, a shekara ta 1994, ta kammala sharia´ar Kalan Theoneste Bagosora, ɗaya daga mutanen da ake ɗauka a matsayin kanwa uwar gami a wannan rikici.

Tun shekara ta 2002 kotun ta fara wannan shari´a, ba tare da yanke hukunci ba.

Kalan Bagosora, da sauran manyan sojoji 3 na ƙasar Rwanda da ake zargi da hannu a cikin wannan ta´asa, sun bayyana wa kotu cewar, ƙage ne ake masu.

Alƙali mai gabatar da shari´a, ya buƙaci ɗaurin rai da rai, ga wannan sojoji 4, to saidaia na sa ran yanke hukuncin ƙarshen a shekara mai zuwa.

Binciken da Majalisar Ɗinkin Dunia ta gudanar, ya gano cewar,Kissan kiyasun da ya wakana a Rwanda, ya hadasa mutuwar mutane dubu ɗari 8, daga ɓangarorin Hutu da na Tutsi.