1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun da ke shari’ar tsohon shugaban ƙasar Iraqi, Saddam Hussein, ta yanke masa hukuncin kisa a zaman da ta yi yau a birnin Bagadaza.

November 5, 2006
https://p.dw.com/p/BudJ

Ba da daɗewa ba ne kotun da ke yi wa tsohon shugaban ƙasar Iraqi, Saddam Hussein shari’a, ta yanke masa da wasu muƙarrabansa guda biyu hukuncin kisa. Kotun, mai samun ɗaurin gindin Amirka, wadda ta yi zamanta yau a birnin Bagadaza, ta ce ta sami Saddam ɗin ne da laifin ba da umarnin yi wa wasu ’yan ɗariƙar shi’iti ɗari da 48 kisa a garin Dujail a shekarar 1982, bayan wani yunƙurin halaka shi da aka yi.

Sauran muƙarraban Saddam Hussein da aka yanke wa hukuncin kisan su ne tsohon shugaban ƙungiyar leƙen asirin Iraqin, Barzan al-Tikriti da kuma tsohon babban jojin ƙasar Awad Hamed al-Bander.

Kotun ta kuma yanke wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Iraqin, Taha Yassin Ramadan hukuncin ɗauri na rai da rai, sa’annan ta yanke wa wasu tsoffin jami’an gwamnatin ƙasar guda uku hukuncin ɗauri na shekaru 15 a gidan yari. Ɗaya daga cikin waɗanda ake yi wa shari’ar, Mohammed al-Azawy, ya sami kuɓuta. Kotun ta ce ba ta same shi da wani laifi ba. Nan take kuma aka sako shi. Manyan jami’an kotun dai sun ce Saddam na da izinin daukaka ƙara game da hukuncin, amma idan kotun jin ƙararsa ta amince da hukuncin, to za a aiwatad da shi ne a cikin kwanaki 30.