1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun koli a Iraqi ta amince da hukuncin kisa kan Saddam Hussein

December 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuWN

Babban mai bada shawara kan harkokin tsaro a Iraqi Mowaffag al-Rubaie ya bada sanarwar cewa wata kotun daukaka kara a kasar ta amince da hukuncin kisa da aka yankewa tsohon shugaban Iraqi saddam Hussein.

Al Rubaie yace kotu ta amince da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa da aka yankewa Saddam a na ranar 5 ga watan nuwamba.

An dai yanke wannan hukuncin ne bisa zargin kisan mutane 148 a 1982 bayan wani yunkuri na kashe Saddam da jamaar kauyen Dujail sukayi.

Alkalin kotun yace ya kamata a aiwatar da wannan hukunci na kisa cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Game da mataimakin Saddam kuwa,Taha Yassin Ramadan alkalin kotun Arif Shaheen,yace hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa yayi sauki saboda haka a cewarsa an maida batun ga babbar kotun kasar domin sake duba shariar farko da aka yanke.