1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun mussamman a kan mutuwar Hariri

Yahouza S.MadobiMay 31, 2007

Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia ya girka kotun mussamman domin bincike a kan mutuwar Rafik Hariri

https://p.dw.com/p/BtvT
Hoto: AP

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya kada ƙuri´ar amincewa da girka kotun mussaman da zata gudanar da buincike ta kuma hukunta masu lefi, a kissan gillar da a aka yi wa tsofan Praministan Libanon Rafik Alhariri.

Idandai aba a manta ba a watan februaru ne na shekara ta 2005 wasu yankunar bakin wake su ka kai hari a tsakiyar birnin Beyruth, wanda a na take ya hallaka Rafik Hariri tare da ƙarin wasu mutane 22.

Har ya zuwa yanzu an kasa tantance masu alhakin wannan kissa, saidai binciken farko da komitin Majalisar Dinkin Dunika ya gudanar ya nunar da cewa ƙasar Syria na da hannu acikin wannan kissa, zargin da hukumomin Damaskus su ka ƙaryata.

A sakamakonkuri´ar da kasashe 15 membobin komitin sulhu su ka kada, 10 su ka a mince da girka kotunta mussaman a yayin da raguwar 5 su ka nuna adawa.

Wannna ƙasashe sun haɗa da Russia Sin Afrika ta kudu, Indonesia, da Qatar.

Jikadankasaer France a Majalisar Ɗinkin Dunia, De la Sabliere ya bayyana hujojin sa, na amincewa da amincewa da daukar wannan mataki.

„Komitin Sulhu ya yanke wannan shawara, kamar yadda gwamnatin Libanon ta bukata.

Sannan Komitin na kashedi, ga dukkan masu buƙatar hadasa fitina a Libanon“.

Wannan ra´ayi ya zo daidai da na mataimakin ministan harakokin wajen Libanon Tarek Mitri, wanda ya jinjina ma komitzinsulhu.

Shi kuwa jikadan Russia a Majalisar Dinkin Dunia, Vitaly Tchourkine,ya nuna adawa da girka wannan kotu:

„Wannan ƙuduri, da aka ɗauka zai mayar da hannun agogo baya, ga ci gaban neman haske a cikin al´amarin, kuma kamar yadda na riga na bayyana,bai kamata a samu cikas ba ,a cikin binciken da aka fara.“

Shima jikadan kasar Syria a Majalsar ya yi Allah wadai da ɗaukar wanan mataki,wanda a tunanin sa ba shi da wani anfani ga ƙasar Libanon.

To saidai ya zuwa yanzu ba a tantantace ƙasar da za a girka cibiyar wannan kotu ba, amma ana ambata ƙasashe kamar su Syprus, Italia , ko kuma Hollande.

Sakatare Jannar an Majlisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Libanon zai ƙayyade ranar da kotun zata fara gudanar da ayyuka.