Kuba: Karshen zamanin iyalan Castro
A wata rayuwar da babu Castros 'yan Kuba da yawa suke iya tuna wani. Tun daga ranar 19.04.2018 a karon farko babu sunan Castro a shugabancin kasar. Kimanin shekaru 60 'yan uwan juna suka mulki kasar da karfin tsiya.
1959 - 'Yan juyin-juya hali sun yi nasara
'Yan tawaye tare da Fidel Castro suna ta dannawa, bayan da a watan Janairu shugaban kama karya Fulgencio Batista ya tsere. Sai daga baya ne Amirka ta samu labari, amma kafin nan tuni 'yan juyin-juya halin suka kaddamar da tsarin kawo sauyi. Shugaban kasar Amirka Dwight D. Eisenhower, ya umarci CIA su kifar da gwamnatin Castro da kuma su maye gurbinta da wani dan amshin shatan Amirka.
1960 - Kishin kasa da kuma kara kusanci da Tarayyar Soviet
Eisenhower ya haramta sayar da dukkan haja i zuwa Kuba in ban da abinci da magunguna inda ya sa kahon zuka kan shugabannin. Kuba ta kara rikidewa bayan ganin gaba ta karu da Amirka, inda suka karfafa hulda da Tarayyar Soviet. Nan ta hagu ana iya ganin Fidel Castro tare da ministocinsa lokacin jana'izar mutanen da wata fashewa ta hallaka, abin da Kuba ta dora alhaki kan CIA da hadda sawa.
1961 - Yunkurin mamaya
Sabani tsakanin Amirka da Kuba ya karu, inda a ranar 03.01.1961 Amirka ta yanke hulda da Havanna. A watan Afrilun shekarar bisa taimakon CIA wasu 'yan kasar Kuba mazauna kasashen waje suka dira a gabar ruwan kasar, da nufin kifar da gwamnatin Fidel Castro. Wannan yunkurin mamaya an murkushe shi cikin kwanaki uku.
1962 - Kololuwar yakin cacar-baka: Rikicin Kuba
1960 jagoran gwamnatin Tarayyar Soviet na lokacin Chruschtschow ya ce: "bani da masaniya ko Fidel dan kwaminisanci ne, amma ni ma daya ne cikin 'yan a mutun Fidel." Tarayyar Soviet ta karfafa tsaron Kuba inda ta girke rokoki bakin tekun kasar ta Kuba, abin da aka yi wa lakabi da "Rikicin Kuba". An kawo karshen tashin hankalin cikin kwanaki 13 bisa tattaunawar sirri tsakanin Moscow da Washington.
1971 – Fidel Castro a Chile
Yunkurin kifar da gwamnatin Kuba ya karfafa wa masu tsatsauran rayi a Latin Amirka. Inda ake koyi da juyin-juya hali. An dai maida Kuba saniyar ware a Latin Amirka, amma kuma sannu a hankali masu ra'ayin rikau suka yi ta kafa kungiyoyin juyin-juya hali a yankin. A shekara ta 1971 Castro ya samu tarba daga shugaban Chili Salvador Allende mai ra'ayin gurguzu. (Hoton dama)
1998 – Ziyarar Fafaroma na farko
Fafaroma Pius XII a shekrar 1941 ya harmta wa dukkan mabiya Katholika taimaka wa 'yan kwaminisanci. Bisa wannan dalilin Castro ya fice daga darikar Katholika. Shekaru bayan kawo karshen yakin cacar baka, yanzu lokaci ya yi na maido da hulda. 1996 Castro ya ziyarci Fafaroma Johannes Paul II. Shekaru biyu bayan haka ya sake wata ziyarar. Bakon da tarihi bai mantawa da shi.
2002 - Fidel Castro da Jimmy Carter na wasan Baseball
Tun shekarar 1962 da Amirka ta haramta kasuwanci ga Kuba, ba ka safai aka samu walwala tsakanin Washington da Havanna. Daya cikin lokacin da aka samu sassauci shi ne ziyarar Jimmy Carter a 2002. Sai dai kokarin inganta kusancin kasashen ya ci tura.
2006 - Fidel da Hugo
Tun shekarun 1990 karfin Kuba ya fara dushewa a yunkurin yada juyin-juya hali. Bayan kawo karshen shingen da ke tsakanin gabas da yammacin Turai, haka ma akidar gurguzu ta fara kawo karshe a Latin Amirka. Sai dai kuma a Venezuela babban abokin Castro ya dare mulki. Hugo Chavez ya ingiza juyin-juya hali a Boliviya yayin da Kuba kuma ta ba da agajin a bangaren tattalin arziki.
2006 - Sauyin mulki
Tsufa ta tilasta wa Fidel Castro, mika mulki. A shekarar 2006 ya mika mulki ga kaninsa Raúl. Wata alamar cewa babu wani babban canji a Kuba. Duk da irin ci gaba da aka samu ta bangaren ilimi da kiwon lafiya, 'yan kasar sun dandana kudarsu: ta bangaren tauye hakki da rashin izinin fadin albarkacin baki tare da muzgunawa jama'a
2014 - Guguawar Sauyi
Raúl Castro da Barack Obama sun yi wa duniya ba-zata a ranar 17.12.2014:Sun yanke shawar mai da hulda tsakanin kasashen biyu da kuma sakin fursunonin siyasa. bisa haka Obama ya sassauta takunkumin karya tattalin arziki. Sai dai wannan guguwar sauyin da dan karamin lokaci ne. A karkashin shugaba Donald Trump huldar ta fara tsami cikin gaggauwa.
2016 - Fidel Castro ya mutu
Sau tari an sha rade-radin mutuwar Castro shi ya sa wasu ma ba sa damuwa da labarin: Domin dubba labarai aka bayar na mutuwar Fidel Castro, bayan shekara sai ya fito. To amma ranar 25.11.2016 jama'a sun kulle shaguna da wuraren shan barasa, yayin da suka samu labari kan titunan Havannas. Domin daga karshe dai a wannan karon Fidel Castro ya yi mutuwar gaske, domin wannan karon bai sake bayyana ba.
2018 – Magajin iyalan Castro
Bayan shakaru 10 shi ma Raúl na son sauka daga mulki, don haka iyalan Castro sun bar mulki. Majalisar dokokin Kuba a ranar 19.04.2018 sun zabi shugaban da sunansa babu Castro a karon farko cikin shekaru kusan 60. Babban dan takara dai shi ne Miguel Díaz mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Raul, (Hoton sa a dama). A bangaren tsarin siyasar kasar dai ana ganin babu sauyin da za a samu.