1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuba: Zaben gyaran sabuwar majalisar wakilai

Zainab Mohammed Abubakar
March 11, 2018

Al'ummar Cuba sun gudanar da zaben daga matsayin sabon shugaban kasa, matakin da ke zama na farkon irinsa a tarihin Kubar cikin kusan shekaru 60, ba tare da iyalin Castro.

https://p.dw.com/p/2u7ni
Kuba | Präsident Raul Castro
Hoto: Getty Images/AFP/J. Beltran

A wannan Lahadin ce al'ummar Kuba ke gudanar da zabe don gyaran sabuwar majalisar wakilan kasar, a wani gagarumin yunkuri na daga matsayin sabon shugaban kasa, matakin da ke zama na farkon irinsa a tarihin Cubar cikin shekaru 60, a wajen iyalin Castro.

Sabbin 'yan majalisar dokokin ne ake saran za su zabi mutumin da zai gaji shugaba Raul Castro mai shekaru 86 da haihuwa, idan ya yi murabus a wata mai kamawa.

Castro ya kada kuri'arsa a gunduwar Santiago de Kuba da ke yankin kudu maso gabashin kasar, a yayin da mataimakinsa kuma wanda ake ganin zai gajeshi Miguel Diaz-Cane, ya yi nashi zaben a gunduwar Santa Clara da ke tsakiya.

A shekara ta 2006 nedai Raul Castro ya karbi ragamar mulkin kasar daga dan uwansa mara lafiya Fidel Castro, wanda ya mulki Kuban tun bayan kifar da gwamnati a shekara ta 1959.

Kimanin Cubawa miliyan takwas ne ke kada kuri'ar gyara majalisar wakilai 605, domin tabbatar da daidaito a wakilcin kasar.