1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudurin janye dakarun Amurka daga Iraki

April 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuN3

Duk da barazanar shugaba George W Bush na Amurka na hawan kujerar naki,wakilan majalisar kasar daga jammiyyar Democrats sun gabatar da kudurin kudi na gaggawa akan kasar Iraki,wanda ya hadar da shirya waadin janye dakarun Amurkan daga wannan kasa.Kudurin Kudin wanda ya kunshi kimanin dala billion 120 na dalan Amurkan ,wanda zaayi amfani dasu wajen fara janye dakarun Amurkan daga cikin Iraki,wanda kuma bazai shige ranar 1 ga watan oktoba na wannan shekara ba,kana a kammala ranar 1 ga watan Afrilu.

Dakarun Amurkan dai guda tara ne suka rasa rayukansu jiya a Irakin,ayayinda wasu 20 suka jikkata sakamakon tashin wani Bomb a yankin arewacin kasar.