1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudurin kungiyar kare hakkin jamaa ta Mdd akan Darfur

March 30, 2007
https://p.dw.com/p/Btvu
Halin Rayuwa a Darfur
Halin Rayuwa a DarfurHoto: AP

Majalisar kare hakkin biladama ta majalisar dunkin duniya ayau,ta sake karfafa matsin lambarta adangane da halin da ake ciki a lardin Darfur,sai dai bata zargi gwamnatin Khartum da yawan zubar da jini da wasu miyagun laifuka na cin zarafin mutane da akeyi a yankin ba.

Kudurin da dukkan wakilan kasashe 47 dake majalisar kare hakkin jamaan ,suka amince da shi ,na bayyana damuwa matuka dangane da cigaban cin zarafin mkutane da akeyi,wanda ya sabawa dokar kasa da kasa a lardin na Darfur.

Kudurin wanda ya samu amincewa abayan kai ruwa rana na kwanaki da dama tsakanin kasashen turai da takwarorinsu na Afrika,ya bada umurnin majalisar ta nada hukumar bincike batutuwan take hakkin jamaa da suka hadar da cin zarafi da azabtarwa da cin mutuncin mata da akeyi a lardin darfur,domin sanin iyakar yadda gwamnatin khartum take darajawa dokar kasa da kasa,tare da gabatar da rahoto a watan yuni.

Jakadan jamus wadda kasarsa ce take rike da zagayen shugabancin kungiyar tarayyar turai,Michael Steiner ya bayyana wannan tattaunawa da kasancewa babbar nasara a bangarensu

“Wannan zartarwa da mukayi babban nasara ce wa kungiyar Eu,kuma nasara ce wa Afrika,kana babbar nasarace itama a bangaren majalisar kare hakkin jamaa,kuma muna fatan cewa hakan zai kasance nasara wa suma alummomin lardin na Darfur”

Sama da mutane dubu 200 nedai suka rasa rayukansu a wannan rikici daya ritsa da yankin na darfur,ayayinda wasu milliyan biyu da rabi suka kaurace daga matsugunnensu zuwa gudun hijira,da barkewan rikicin a 2003.

To sai dai wa Directar kungiyar kare hakkin biladama ta human right watch Peggy Hicks,babu alamun cimma wata madafa a wannan yunkuri nasu.

“Ina ganin wannan kuduri da ak cimmawa bazai iya cimma burinsa kamar yadda ake sa zato ba,sai dai zamuyi iyakar kokarin mu na ganin cewa muma mun bada tamu irin gudummomowa wajen warware wannan rikicin”

Daga cikin takardun da tawagar binciken zasuyi laakari dasu dai,zasu hadar da rahotan da komitin binciken rikicin na Darfur ya gabatarwa majalisar a farkon wanmnan wata da muke ciki,rahotan da ke zargin gwamnatin khartum da hannu cikin irin badakkalar da darfur ya fada ciki.

Gwamnatin Sudan din dai ta karyata wadannan zarge zarge da Amurka da wasu kasashe keyi mata,inda ta dangana wannan kisan kiyashi da kungiyoyin yan adawa wadanda suka ki rattaba hannu a yarjejeniyar suhu da aka cimawa a shekara ta 2006 data gabata.kaszalika tana cigaba dayin kunnen uwar sheku dangane da kiraye kiraye da ake mata na amincewa da tura dakarun kiayye zaman lafiya na mdd zuwa cikin kasar domin tallafawa na kasashen Afrika kimanin dubu 7 dake fama da karancin kayyayakin aiki.