1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudurin rage harajin masana'antu a Nigeria

September 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuB4

Shugaba Umaru Musa Yar’adua na tarayyar Nigeria yayi alkawarin gabatar da sabon kuduri kann biyan haraji,wanda zai kawo karshen ninkin harajin da masana’antu ke biya ,tare da taimakwa masu kamfanonin kansu ,wanda inji shi ,shine tubalin bunkansar wannan kasa mai yawan Al’umma a nahiyar Afrika.

Yar’aduwa wanda ya haye karagar mulkin Nigeria a karshen watan mayu,yayi alkawarin farfado da tsarin sakarwa harkokin kasuwanci mara da aka kaddamar a 2003,inda yace gwamnatinsa zata sake nazarin kudurin yiwa biyan haraji garon bawul,wadda gwamnatin data gabata ta tsara amma bata zartar dashi a matsayin dokar kasa ba.Shugaban Nigerian wanda yake wadannan bayanan wa shugabannin kamfanoni a Abuja,ya tabbatar da gabatar da wannan kuduri gaban majalisar dokoki domin mahawara.Kamfanonin dai sun koka dangane da tsari na yanzu,inda sukan biya kudaden haraji fiye da sau guda a shekara.