1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kulab mafi Daukaka a Turai

Abba BashirJune 5, 2006

Real Madrid shi ne Kulab mafi daukaka a Turai

https://p.dw.com/p/BvVP
Carlos da Figo
Carlos da FigoHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Bala Nuhu , mazauni a garin Difa dake Jamhuriyar Nijar. Malamin ya ce wane kulab ne mafi daukaka a Nahiyar Turai wanda kuma ya fi yawan samun nasarar cinye kofin gasar kwallon kafa na Nahiyar Turai?

Amsa : To Malam Bala wannan nasara dai ta tafi ga shahahararen Kulab dinnan na Real Madrid da ke Kasar Spain, wanda aka kafa a shekarar 1957 kuma ya samu nasarar lashe gasar cin kofin kwallon kafa na Nahiyar Turai har sau tara (9). Kulob din dai ya samu wadannan nasarori ne a shekarar 1955-56, 1956-57, 1957-58, 1958-59, 1959-60, 1965-66, 1997-98, 1999-2000, da kuma 2002.

Kulub din na Real Madrid dai bawai a Nahiyar Turai kawai ba, a na ganin a Duniya ma gabadaya shine Klub din da ya fi kowanne gawurta, idan dai ana batun kwallon kafa.Domin kuwa Kulab din ya na da tarihin samun nasarori a gasanni daban-daban ta kwallon kafa a Duniya. A tarihi Kulab din ya lashe gasar League-League watau wasannin Klub-Klub na cikin gida na kasar Spain har sau (28), kuma sau (17) ya na samun nasarar cinye kofin kwallon kafa na kasar ta Spain.

Idan aka koma batun yan wasan da suke bugawa wannan Kulab wasa kuwa, sai ace mafiya yawan fitattun yan wasan da suka yi suna a Duniya ko kuma suke kann yin sunan, sune suke tattare a wannan Kulab na Real Madrid. Na farko dai dan wasa mafi tsada a Duniya wato Zinedane Zidane dan wannan Klub ne.Bayan sa kuma akwai irin su Robator Carlos (dan kasar Brazil), da Ronaldo (dan kasar Brazil) da David Beckham (dan kasar Ingila), da Borja Fernandez (dan kasar Spain) da Carlos Diogo (dan kasar Uruguay), da Pablo Garcia (dan kasar Uruguay) da Thomas Gravesen (dan kasar Denmark), da Guti (dan kasar Spain) da Raul Gonzales (dan kasar Spain) da dai sauran su.