1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiya na koya wa guragu sana'o'i a Kano

Abdurahman kabir daga Kano/ MABJuly 13, 2016

Kungiyar nakasassun da Polio ya gurganta a kano na Koya wa matasanta sana'ar kera kekuna da hada babura da motoci na guragu don maganin zaman kashe wando.

https://p.dw.com/p/1JOLv
Nigeria Polio Rollstühle
Hoto: DW/M. Aminu Hussaini

A bangaren wani gida da kungiyar ta guragu take haya ne matasanta ke kera kekuna da take baje kolinsu a harabar gidan. Ibrahim Abubakar wanda sai a shekara mai zuwa zai kammala makarantar sekandare ne yake jagorantar sauran matasa biyar da suka dukafa wajen yin aiki gadan-gadan.

Yayi kira ga sauran guragu da su zo su koyi sana'a, saboda tuni wasu daga cikin matasa da suka ci gajiyar horon suka kafa nasu wuraren. Ya ce duk nakasasshen da "Ya zo zamu koya masa sana'a:"

Baya ga kekuna akwai babura na guragu da lilo na wasan yara, wadanda matasan kungiyar nakasassu ke kerewa. A cewar shugaban reshen kungiyar na jihar Kano, Alhaji Aminu Inuwa Tudunwada, koyan darasin rayuwa da ya hanashi karatun firamare ne ya sashi kama sana'a.

Nigeria Polio Rollstühle
Kekunan guragu na daga cikin abubuwan da matasan ke kerawaHoto: DW/M. Aminu Hussaini

Ya ce: "Rashin keken guragu ne ya hanani karatun firamare." Saboda haka ne ya kudiri aniyar share wa matasan da ke cikin wannan hali hawaye.

Kungiyar nakasassun da Polio ya gurgunta na kokarin ganin matasanta sun yi karatu tare da kama sana'a. Sai duk da wannan kokari ta koka da rashin samun gwarin gwiwa daga mahukunta da ma sauran jama'a.