1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Alkalai a Nijar ta nemi minista ya yi murabus

Abdoulaye Mamane Amadou
February 25, 2017

Yanzu hakan dai hankali ya karkata ga makomar ministan kudin kasar batun da sannu a hankali ke cigaba da daukar sabon salo yadda 'yan adawa a kasar su ke kara matsa kaimi.

https://p.dw.com/p/2YG9J
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Hoto: DW/M. Kanta

A Jamhuriyar Nijar a ranar Asabar nan ne hadadiyar kungiyar alkalai ta kasar ta kira wani taron manema labarai inda a ciki ta bukaci ministan kudin kasar Hassoumi Masasoudou da ya yi murabus ya kuma gurfana a gaban kuliya domin wanke kansa bisa zarge-zargen da a ke masa na cewar ya na da hannu a cikin badakalar salwantar makuddan kudade kimanin miliyan dubu 200 a cikin wani asusun ajiya a kasar Dubai.A farkon makon jiya ne dai wata jarida mai zaman kanta ta ambaci badakalar tare da ambata sunan ministan da hannu dumu-dumu a cikin zargin da ministan ya karyata ya na mai cewar shaci fadi ce kawai irin ta 'yan jarida,