1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Alqaeda ta lashi takobin kai manyan hare hare

June 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuuT

Kungiyar Aqaeda a Iraki a yau lahadi ta lashi takobin kai manyan hare hare wadda tace zasu gurgiza abokan gabanta,bayan kashe shugabanta na Iraqi Abu Musab alzarqawi.

Cikin wani sako ta yanar gizo,kungiyar tace manyan jamianta sunyi taro bayan kashe Zarqawi domin tattauna hanyoyin da zata maida martani tare kuma da sabunta mubayaarsu ga Osama Bin Laden.

Sanarwar tace hare hare da suka shirya kaiwa zasu matukar girgiza abokan gaba tare da hanasu runtsawa,saboda abinda suka aikata.