1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU da rikicin Dafur

May 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buzq

A yayin da jamiaí masu shiga tsakani ke cigaba da kokari domin gano bakin zaren warware rikicin yankin Dafur tsakanin gwamnatin Sudan da yan tawaye, babban jamiín gwamnatin Amurka, kuma mukaddashin sakatare a maáikatar harkokin waje Robert Zoellick ya bi sahun jamián kungiyar gamaiyar Afrika a birnin tarayyar Nigeria Abuja domin cimma yarjejeniyar zaman lafiyar, kafin cikar waádin da aka debarwa bangarorin biyu wanda zai kare a daren Talatar nan. A na ta bangaren gwamnatin Sudan ta amince da daftarin yarjejeniyar mai shafi 85 to amma bangarori uku na yan tawayen Dafur, sun ce ba za su sanya hannu a kan yarjejeniyar ba saboda abin da suka kira rashin daidaito a rabon madafan iko da da rabon arzikin kasa da kuma shaánin tsaro. Tun da farko jamiín kungiyar gamaiyar Afrika Salim Ahmed Salim ya bukaci yan tawayen a cikin wata sanarwa da su kawar da banbance banbancen dake tsakanin su, su rungumi shirin zaman lafiyar. Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Robert Zoellick da sakatariyar hukumar bada taimakon jin kai na Britaniya Hilary Benn sun gana da bangarorin yan tawayen a kokarin samun masalaha ta cimma yarjejeniyar zaman lafiyar. Manazarta na baiyana cewa sanya baki da jamián na Amurka da Britaniya suka yi zai taimaka wajen shawo kann yan tawayen su amince da yarjejeniyar sulhun.