1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU ta baiwa yan tawayen Dafur wáádin makwanni biyu su amince da yarjejeniyar sulhu

May 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuyI

kungiyar gamaiyar Afrika ta bada waádin nan da karshen wannan watan ga kungiyoyi biyu na yan tawayen Dafur su sanya hannu a kan yarjejeniyar sulhun da aka cimma ko kuma su fuskanci takunkumin majalisar dinkin duniya. Bayan tsawon lokaci na shawarwarin sulhun wanda kungiyar gamaiyar Afrika ta dauki nauyin gudanarwa a Nigeria, kungiya daya ce kawai daga cikin kungiyoyin yan tawayen uku ta sanya hannu a kan yarjejeniyar a ranar 5 ga watan Mayu tare da gwamnatin Sudan da nufin kawo karshen fadan da ya hallaka rayukan dubban jamaá a yankin . Shugaban kungiyar gamaiyar Afrikan Alpha Umar Konare ya bukaci reshen kungiyar yan tawayen SLA dake karkashin jagoranci Abdel Wahid Mohammed Nur da takwarar ta ta JEM da su sanya hannu a kan yarjejeniyar ba tare da wata togaciya ba. Yana mai gargadin cewa kungiyar AU za ta dauki tsauraran matakai idan kungiyoyin yan tawayen suka yi yunkurin gurgunta shirin zaman lafiyar. Ministan harkokin wajen Nigeria Olu Adeneji kuma shugaban majalisar tsaro da sasanta zaman lafiya na kungiyar gamaiyar Afrika ya ce karin waádin makwanni biyu ga yan tawayen su amince da yarjejeniyar wata muhimmiyar dama ce wadda kin yarda da ita zai nuna cewa kungiyoyin biyu na yan tawayen ba su da kudiri na son zaman lafiya. Yarjejeniyar ta haifar da bore a sansanonin yan gudun hijira a Dafur inda suke baiyana cewa bata wadatar ba wajen basu cikakkiyar kariya. Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan yace akwai bukatar dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa su karbi ragamar shaánin tsaro a yankin ba tare da jinkiri ba.