1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU ta yi kira da a amince da sakamakon zaben shugaban Liberia

November 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvLR

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta yi kira da a girmama sakamakon zaben shugaban kasar Liberia, wanda kusan babu shakka zai ba Afirka shugabar kasa mace ta farko da aka zaba. Yanzu da aka kammala kidayar kashi 97 cikin 100 na kuri´un da aka kada, Ellen Johnson Sirleaf masaniyar tattalin arziki da ta yi karatu a jami´ar Havard ta kasar Amirka ta samu kashi 59.4 cikin 100. To sai dai jam´iyar tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar kasar da ya kalubalance ta a zaben wato, George Weah, ta shigar da kara ta na zargin tabka magudin zabe. An jiyo shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Alpha Omar Konare na kira da ´yan takarar da su amince da sakamakon zaben a matsayin abin da al´umar Liberia suka zaba. Konare ya ce duk mai zargin an yi aringizon kuri´u to yabi hanyoyin da doka ta amince da su don neman hakkin sa.