1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Au tace dole Mugabe yaje taron Lisbon

October 6, 2007

kasashen afrika sun jaddada matsayinsu

https://p.dw.com/p/BtuR
Robert Mugabe na Zimbabwe
Robert Mugabe na ZimbabweHoto: dpa

Jami’an diplomasiyya na na kasashen Africa sun cimma matsaya guda na marana shugaba Robbert Mugabe na Zimbabwe baya,adangane da halartan taron hadin gwiwa na kasashen turai da Africa da zai gudana a Lisbon a watan Di samba.

Wani jamii daga headquatar kungiyar gamayyar kasashen Africa dake Adisa baba ,ya bayyana cewar kungiyar na bukatar dukkanin shugabannin Afrikan su halarci taron na Lisbon.

Wannan sanarla dai ya sabawa kalaman ministan harkokin wajen faransa Bernard Kouchner,nacewa gamayyar Afrikan ta amince da kiran Mugabe daya janye daga halartan wannan taron na kasar Portugal.

Mai shekaru 83 da haihuwa,shugaba Robbert Mugabe na fuskantar suka da matsin lamba daga kasashen ketare ,musamman na turai a dangane rigingimu na siyasa da take hakkkokin jama’a da kasarsa ke fama dasu,banda uwa uba durkushewar tattalin arzikin kasar.

Premiern Britanna Gordon Brown dai ya fito karara ya nunar dacewa,zai kauracewa wannan taron idan har shugaban Zimbabwe zai halarta.

A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus wadda ta kammala rangadin aiki a kasar Africa ta kudu a jiya,wanda kuma Zimbabwen nada daga cikin muhimman batutuwa da suka tattauna akai,tace kowane shugaban Africa nada yancin halartan wannan muhimmin taro..

“Merkel tace an dauki shekaru da dama ba tare da cimma gudanar da taro tsakanin Africa da turai ba.Kuma kamar yadda na fada a kasa ta jamus ,ina nan kan raayina na cewar a gayyaci dukkannin shugabannin Africa zuwa wannan taro.Domin anan ne kowane shugaba zai yi bayanan sa a bainar sauran,wadanda zasuyi nazari tare da mayar da martaninsu.Adangane da hakane nake jaddada cewar kowane shugaba yana da yancin halartan wannan taro”

Shima komitin suhu tare da tabbatar da tsaro na kungiyar ta Au ya bayyana Zimbabwe da kasancewa daya daga kasashen nahiyar Africa,kuma dole ne a darajawa akidojinta na cikin gida,duk da irin matsaloli da take fuskanta.Yace sun yi kira ga Mugabe daya tuntubi yan adawar kasarsa,domin basa tsoma baki a harkokin cikin gida na kasashe,sai dai idan akwai mummunan yanayi na kisan kiyashi ko tashe tashen hankula.

Jamiin Komitin yace ai bawai a Zimbabwe kadai ne baa darajawa harkokin democradiyya ba,akwai kasashe kamar Togo da Niger dake da matsaloli makamancin wannan,Zimbabwe dai nata ya fito fili ne domin tana da matsala da uwargijiyarta Britanna.

A bangarensu shugaban hukumar gudanrwa na Au Alpha Omar Konare da shugaban kungiyar na yanzu John Kufour,sun jaddada manufofinsu na cewar dole ne a gayyaci dukkannin shugabbanin Africa zuwa taron,matukar ana neman cimma nasara.