1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar yin sulhu da Boko Haram

Uwais Abubakar Idris /LMJAugust 5, 2015

A Najeriya al'umma na mayar da martani bisa batun da cibiyar samar da bayanai a kan rigingimu ta yi na cewar wasu 'yan kungiyar Boko Haram sun tuntube ta da nufin neman sulhu.

https://p.dw.com/p/1GAOA
'Yan Ta'addan Boko Haram
'Yan Ta'addan Boko HaramHoto: picture alliance/AP Photo

Duk da cewa labarin yunkurin sulhu daga bangaren kungiyar ta Boko Haram lamari ne da ke kamshi tamkar turare dan goma ga al'ummar Najeriya saboda kosawar da kowa ya yi kan hakan, bayanan da suka fito daga kungiyar na zama abin da ake taka tsan-tsan a kansa. Ko menene sahihancin bayanan da cibiyar ta yi? Tsohon kwamandan mayakan sama na Najeriya Yusuf Anas shi ne sakataren gudanarwar kungiyar ga kuma abin da yake cewa:

"Sanin cewa ana neman maslaha a kan abubuwa don haka wasu daga cikinsu suka tuntubi cibiyarmu domin sanin ko da gaske gwamnatin na son a yi sulhu. Muna kokarin tantance wadanda suka tuntubi cibiyar tamu, muna fatan nan ba da jimawa ba zamu tabbatar da cewa sahihan mutane ne wadanda gwamnati za ta iya tattaunawa da su."

Shugaba Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

An sha yin ruwa kasa na shanyewa

A baya dai an sha ganin yunkuri irin wannan daga kungiyoyi da ma wasu mutane da ake ganin suna da tasiri a idon jama'a amma kuma daga karshe kungiyar ta ce ba ta da masaniya kan batun. Wannan ya sanya jefa tambayoyi mabanbanta musamman na ko cibiyar ta samar da bayanai a kan rigingimu na da karfi ko martabar da za ta iya shiga tsakani a irin wannan rikici? Malam Kabiru Adamu kwararre ne a fanin tsaro a Najeriyar ga kuma abin da ya ke cewa:

"Irin halin da muke ciki duk wanda ya ce ga gudummawar da zai bayar sai mu yi mashi kyakkyawan fata, ni a fahimtata wanda ya gabatar da kansa ya yi wannan jawabi tsohon soja ne, suma sauran ‘yan kungiyar suna da alaka da harkar tsaro ko kuma sojoji, to za mu iya yi musu kaykkyawan zato na cewa suna da masaniya a kan harkar ta'addanci da kuma irin hanyoyin da ake bi wajen tantance wanda ya gabatar da kansa ya ce yana da alaka da ta'addanci, mataki na farko shi ne tantance ainihin wadanda suka gabatar da kansu kuma suka ce su na da alaka da kungiyar."

Bukatar yin taka tsan-tsan

Duk da cewa batun sulhu da masu kai hare-hare a Najeriyar na zama yanayi na tamkar wanda ruwa ya ci ko takobi aka mika masa zai kama, ga Birgediya Janar Mansir Dan Ali mai ritaya kwararre a fanin tsaro a Najeriyar akwai bukatar yin taka tsan-tsan inda ya ce:

Masu fafutukar ganin an sako wadanda Boko Haram ta sace
Masu fafutukar ganin an sako wadanda Boko Haram ta saceHoto: Reuters

"Ni a ganina abi a hankali domin wata kungiya da ta taso wacce zan iya cewa sabuwa ce bai kamata ace ta yi kane-kane a kan wannan lamari ba, a baya ai an yi irin wannan ya yiwu a gaba za'a sake yin hakan. Don haka sai an yi a hankali sannan a gane su waye ke neman a yi sulhu da su kuma wadanne mutane ne zasu shiga tsakani wajen wannan sulhun."

A yayin da ake ci gaba da bibiyar abin da ka iya biyo baya daga wannan batu da cibiyar ta samar da bayanai a kan rigingimu ta Najeriya ta samar, abin zura idanu a gani shi ne ci gaban da za'a samu daga bangarenta da ma gwamnatin Najeriyar karkashin shugaba Muhammadu Buhari da ta ce kofofinta a bude suke na yin sulhun da 'ya'yan kungiyar.