Kungiyar EU na dab da cimma matsaya da Kasashen Afrika
November 12, 2015Talla
Shugabanin kungiyar Tarayar Turai na shirye-shiryen kaiwa ga cimma wata matsaya akan wasu kudirori biyar da takwarorinsu daga nahiyar Afrika wajen bayar da tallafin kudade don kawar da matsalolin da ke janyo matsalar 'yan gudun hijira zuwa Turai.
Dukkanin bangarorin biyu na fatan ganin ta samu tagomashin kasashen tare da yin aiki tukuru a tsakaninsu wajen dakile safarar mutane da bazuwar 'yan gudun hijira gami da fadada tallafin taimako ga kasashen da matsalar tafi kamari.