1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta bukaci Libya ta mika mata jami'an kiwon lafiya na Bulgaria

July 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuG1

Kungiyar taraiyar turai ta bukaci kasar Libya da ta maiyarda maaikatan jiyyan 6 zuwa kasarsu bayan sauya masu hukuncin kisa da akayi zuwa daurin rai da rai.

Wannan shawara da majalisar koli ta sharia a Libyan ta yanke ya zo ne yayinda iyalan yaran da abin ya shafa sunce sun janye neman hukuncin kisa ga wadannan maaikatan kiwon lafiya bayan an biya su diyyar dala miliyan guda kowannensu.

Ministan harkokin wajen Bulgaria Ivaylo Kalfin yace wannan hukunci wani babban mataki daya dace sai dai ya bukaci a mika su ga gwamnatin kasar Bulagria a nashi bangare takwaransa na Libya Abdel Rahman Shalgam yace Libya zata duba batun mika jamian na kiwon laffiya wadanda suke daure a kasar tun 1999.

Hukumar taraiyar turai itama ta bukaci a mika wadannan mutane ga KTT ba tare da bata lokaci ba.