1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta sanya takunkumi ga masu hannu a juyin mulki a Burundi

Yusuf BalaOctober 2, 2015

A cewar mujallar kungiyar ta EU Janar Ngendakumana na daga cikin masu yin karantsaye ga yunkurin sulhunta rikicin siyasa a kasar.

https://p.dw.com/p/1Ghww
Burundi Armee General Leonard Ngendakumana
Janar Leonard NgendakumanaHoto: Reuters/J. Akena

Daya daga cikin tsaffin dakarun soji da ya rike mukamin Janar da ya mara baya a shirin juyin mulkin shugaba Pierre Nkurunziza da ya gaza nasara a kasar Burundi a watan Mayu da ya gabata, kungiyar EU ta sanya masa takunkumi, adaidai lokacin da a ke lalubar hanyoyi na dakile rikici a kasar da ke a Gabashin Afirka.

Janar Leonard Ngendakumana na daga cikin manyan mutane hudu na kasar, da kungiyar EU ta haramta musu shiga daukacin kasashenta 28. Sannan duk abin da suka mallaka na ajiya a bankunan kasashen basu da ikon ta'ammali da su.

A cewar mujallar kungiyar ta EU Janar Ngendakumana na daga cikin masu yin karantsaye ga yunkurin sulhunta rikicin siyasa a kasar sannan yana daga cikin wadanda suka tallafa wajen tada rikici da ma kai hare-hare ta hanyar amfani da makaman gurneti.