1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta yi maraba da umarnin kotun kolin Libya

December 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvF4

Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da umarnin da kotun kolin Libya ta bayar na sake yin shari´ar da ake yiwa ma´aikatan jiyya ´yan kasar Bulgaria su 5 da wani likita Bafalasdine da aka yankewa hukuncin kisa bisa laifin yiwa kananan yara allurar yada kwayoyin cutar HIV. Mai magana da yawun hukumar EU mai kula da harkokin ta na ketare Emma Udwin ta ce rashin tabbatar da hukuncin kisan wani labari ne mai dadin ji. Sannan ta kara da cewa wannan umarni zai ba da damar warware wannan takaddama cikin hanzari. A yau dai ne kotun kolin kasar ta Libya ta dage hukuncin kisan da aka yankewa ma´aikatan jiyya su 5 da kuma likitan daga Falasdinu. Alkalan kotun dake birinin Tripoli sun ce dole a sake zaman sauraron wannan shari´a tun daga tushe.