1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan cirani: Kungiyar EU na neman mafita

Zulaiha Abubakar
June 20, 2018

Shugabanni Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da suka hada da Jamus da Faransa za su tattaunawa a kan batun 'yan cirani a Brussels ranar Lahadin nan gabanin babban taron kungiyar wanda zai gudana a makon gaba.

https://p.dw.com/p/2zxfM
Jean-Claude Juncker
Jean-Claude JunckerHoto: picture-alliance/AP Photo/O. Matthys

Matakin tattaunawar ya biyo bayan kiran da shugaban EU Jean-Claude Juncker ya yi sakamakon yadda batun 'yan ciranin ke yunkurin haddasa rarrrabuwar kai a tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar. Cece-kucen da ya kutso kai a baya-bayan nan shi ne yadda gwamnatin hadakar Jamus ta Angela Merkel ke fuskantar matsin lamba sakamakon ba 'yan gudun hijira sama da miliyan daya mafaka tun a shekara ta 2015, lamarin da har yanzu ya ke cigaba da janyo mata bakin jini daga wasu bangarorin.