1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Hamas ta amince da sasantawa

Zainab A MohammadMarch 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7a

Hamas

Yan kungiyar Hamas masu tsattsauran raayi na Palasdinu sun sanar dacewa zasu canja akidojinsu,bayan lashe zaben yankin ,sai dai babu alamun Hamas din zata nemi sulhuntawa da Izraela.Wadannan kalamai sunzo ne a daidai lokacinda shugaban kungiyar Khalid Meshaal ya kammala ziyarar aikinsa na farko a fadar gwamnati ta Kremlin ta Rasha,inda kuma ya gana da shugaban majamiar Orthodox dake a wannan kasa. Jagoran cocin dai,ya bukaci hamas data tattauna da Izraela.

To sai dai duk da wadannan tausasan kalamai na Hamas,mukaddashin Prime ministan Izraela Ehud Olmert ya fadawa shugaba Vladimir Putin na Rasha cewa,wannan tattaunawar kuskure babba,wanda zai dada bawa yan Hamas din damar lalata wannan kasa ta yadawa.