1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Islamic Jihad taki karabar tayin shiga gwamnatin yankin Palasdinawa

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7L

Kungiyar Islamic Jihad taki karabar tayin da kungiyar Hamas tayi mata na shiga sabuwar gwamnatin yankin Palasdinu.

Shugaban kungiyar Islami jihad Nafez Azzam,ya fadawa manema labarai bayan ganawarsa da jamian kungiyar Hamas cewa,ba zasu shiga gwamnatin Palasdinun ba amma kuma suna masu goyon bayan Hamas a gwagwarmaya da takeyi da kuma kare jamaar yankin.

Tun kafin wannan ganawa dai,kungiyar Islamic Jihad ta baiyana tsoronta cewa,gwamnati karkashin kungiyar Hama zata samu cikas wajen manufofinta,saboda wasu yarjeniyoyin tsakanin hukumar Palasdinu ta baya da Israila,wadanda dukkaninsu kongiyoyin biyu basa goyon baya.

Hamas dai ta ce,duk da kin amincewa da wannan tayin da kungiyar Islamic Jihad tayi,kofa a bude take ga kungiyar ta shiga gwamnatin a duk lokacinda take so.