1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kungiyar matasa kan samar da aiki

January 18, 2017

Wata kungiyar matasa a Jihar Ktsina da ke Najeriya ta dukufa wajen horas da matasa sana'o'i domin kawo karshen zaman banza.

https://p.dw.com/p/2VzIz
Nigeria Selbstmordanschlag 30.07.2014
Hoto: Reuters

A Jihar Katsina da ke Najeriya wasu matasa masu sana'o'in hannu da suka hada da teloli, da kafintoci da masu Walda da masu sana'ar gyaran ruwan fanfo da dai sauransu sun kafa kungiya wadda suka saka mata suna "Katsina Youth Development and Poverty Eradication Iniative" inda suka himmatu a karan farko suka zabo matasa 250 maza da mata suna ba su horo na sati uku kan irin sana'o'in da suka iya kyauta da niyyar dakile zaman kashe wando.

Matasa dai sun yi hangen kafa wannan kungiya ganin irin yadda yan uwansu matasa ke zaman kashe wanda babu sana'o'i alhalin kuma akwai damar yin sana'o'in ya sa suka sadaukar da kansu suna koyar da matasan sana'o'in kyauta a inji jagoran kungiyar Abubakar lawal Mani

"Kungiya ce mai yaki da talauci da samar da ci-gaban matasa a jihar Katsina, mun duba yanayin zamantakewa na rayuwar matasanmu da dama sun gama karatu amma ba su da aikin yi wasu kuma suna da aikin amma ba sa zuwa, da akwai da dama wadanda suke bukatar tallafin a koya masu sana'o'in damin su zamo masu dogaro da kai "
 

Shin ko wadan ne irin sana'o'i ne wadannan matasa ke koyar da yan uwansu? Lawal mani, ya ce akwai dinki na maza da mata da dinkin jikkuna na yara na makaranta da kuma koyar da aikin sabulu na wanka dana wanki.

Wani matashi ya sadaukar da kansa dan koyar da dinki ga wasu matasa:

"Sunana Abdulahi Garba Jani, ni dai tela ne sannan cikin kungiyar nan akwai teloli kuma ance a wannan shiri da aka kaddamar akwai aikin tela da za a koya sai nace to shike nan ba sai ansha wata wahala ba."

Ana bayyana matasa dai a matsayin shuwagabannin gobe kuma kullun ake saran su zamo na gari wanda zama masu dogaro da kai na daga jigon kawo masu natsuwa.