1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Mehdi a Iraqi ta kamme garin Amarah

October 20, 2006
https://p.dw.com/p/BufA

Yan shia karkashin jagorancin Moqtada al Sadr sun kame garin Amarah yau jumaa a wani abinda yan sanda suka baiyana da cewa kangara na karfin hali da suka taba gani.

Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai na Iraqi Yassin Majid ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AP cewa firaminista Nuri al Maliki tuni ya aike da tawagar tsaro ta gaggawa data hada da karamin minista tsaron kasar da wasu manyan jamian maaikatar harkokin cikin gida dana tsaro.

Kakakin maaikatar harkokin cikin gida Karim Khalaf ya shaidawa AP cewa dakarun tsaron Iraqin sun isa wajen garin na Amarah inda yan kungiyar Mehdi suka ragargaza manyan ofisoshin yan sanda guda 3 .

A dai watan agusta ne rundunar sojin Burtaniya ta mika aiyukan tsaron garin hannun sojoji da yan sanda na Iraqi.